Aisha Buhari Ta Soki Shirin Gwamnatin Tarayya Na Rage Fatara

Mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta ce, shirin gwamnatin tarayya na rage fatara da samar da aikin yi ga matasa bai samu nasara ba a yankin arewacin kasar nan.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne lokacin da ta ke tattaunawa da mata a fadar Asorok da ke Abuja a ranar Asabar 25 ga watan Mayu 2019.

A cewar uwargidan shugaban kasar Najeriya, akwai lokacin da ta samu daya daga cikin jagorororin da ke kula da shirin wanda ya tabbatar da mata cewa mata dubu talatin za su amfana da shirin bai wa mata dubu goma-goma a jahar ta,wato Adamawa amma har ya zuwa yanzu babu amo ba labari.

Aisha Buhari tayi  misali da wani dattijo mai shekaru 74 da ta  ganshi a gefen titi a Kano, yana sayar da kayayyaki da ta tambaye shi ko nawane jarin sa ya ce bai wuce dubu uku zuwa hudu ba lamarin da ke nuna cewa da an bashi dubu goma zai bunkasa kasuwancin sa.

Jawabin nata na zuwa ne kwanaki uku bayan da mai bai wa shugaban kasa shawara kan shirin samar da aikin yi Maryam Uwais ke cewa gwamnatin ta kashe sama da naira biliyan dari hudu da saba’in (470bn ) tun farkon fara shirin.

Shirin yaki da fatara da samar da aikin yi ga matasa sun hada da: Shirin Npower da shirin ciyar da daliban makarantun firamare da shirin ba da kudade ga kananan ‘yan kasuwa da sauransu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More