Aisha Buhari tayi kira ga mata da matasa da su zabi Buhari

Matar shugaban kasa, A’isha Buhari tayi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar APC matasa da mata da su zabi maigidanta shugaban kasa  Muhammadu Buhari a zaben mai gabatowa  na  cikin watan Fabarairun 2019.

A’isha Buhari ta yi wannan kiran ne a ranar Asabar 5 ga watan 2019 a lokacin da ta kaddamar da yakin neman zabe  a arewa maso yamma a filin wasan kwallon kafa na Sani Abacha dake Kofar Mata a jahar Kano.

A’isha Buhari ta ce tana goyon bayan jam’iyyar APC ne sakamakon ayyukan da jam’iyyar ta zuba ta taimakon ‘yan kasa wanda gwamnatin maigidanta shugaban Buhari ya kaddamar.

Ta bayyana cewa; a shekarar 2015, jam’iyyar APC ta yiwa al’umma alkawura, ta ce; yanzu ta fito yakin neman zabe ne saboda ta fadawa ‘yan Nijeriya irin nasarorin da jam’iyyar ta samu a tsawon shekarun da take mulki, a cewarta jam’iyyar ta cika wadansu alkawuran da ta yiwa ‘yan Najeriya.

 

Daga cikin alkawuran akwai ciyar da daliban makarantu abinci, shiri N-Power, a inda wadansu dalibai suka samu aiki a karkashin shirin, inda suke samun Naira 30, 000 a duk wata.

Aisha Buhari  ta zayyano batutuwa da dama wanda a cewarta jam’iyyar ta APC sun cika su shiyasa yanzu ta fito domin taya su yakin neman zaben mai gabatowa na 2019.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More