Akwai hadin bakin yan siyasa da Boko Haram a hare-hare Zamfara – Zargin Gwamnatin Jahar

Gwamnatin jahar Zamfara tace ta samu rahotannin kwararru abun dogaro dake nuni da cewa wasu yan siyasa a jahar suna wani yunkuri cikin sirri don hargitsa jahar, sai dai bata ambaci sunayen yan siyasan ba.
 
 
Wani jawabin daga babban darektan harkokin sadarwa na gidan gwamnatin jahar Zamfara Yusuf Gusau, yayi zargin cewa yan siyasan na hada kai da tarwatsattsun yan Boko Haram wajen kaddamar da jerin hare-hare akan bayin Allah.
 
Jami’in yace anyi shirin ne don katse zaman lafiya da tsarin yarjejeniyar da gwamnati mai mulki ta kafa.
 
 
Yan bindiga a halin yanzu sun shiga tsarin yarjejenyar zaman lafiya a Jahar, wanda yayi sanadiyyan sakin yan bindiga da wadanda yan fashin suka sace daga dukkan fannonin rigingimun tsaron da ya addabi jahar a cikin kwanakin.
 
 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More