Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ne sabon sarkin Rano

Gwamnan jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nada Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa a matsayin sabon sarkin Rano.

Kafin nadin na Alhaji Kabiru, shi ne hakimin Kibiya kuma Kaigaman Rano.

Ya maye gurbin margayi Sarkin Rano, Alhaji Tafida Abubakar Ila Autan Bawo wanda ya rasu a ranar Asabar 2 ga watan Mayu da ta wuce bayan ya yi fama da gajeruwar jinya

Sakataren gwamnatin jahar Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya sanar da nadin sabon sakin na Rano a ranar Talata. Babban jami’in gwamnatin ya fitar da sanarwar cewar, an zabi Alhaji Kabiru Muhammadu Inuwa ne a matsayin sabon sarki, daga cikin hakimai uku da suka hada da hakimin Bunkure da kuma Ciroman Rano.

Marigayi Autan Bawo yana cikin sarakuna masu daraja da daya da Gwamna Ganduje ya nada a shekarar 2019.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More