
Alhassan Doguwa ne Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Wakilai
Alhassan Doguwa ne Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Wakilai
Jam’iyyar APC ta zabi dan majalisa mai wakiltar Doguwa/TuduWada na jahar Kano a matsayin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai.
Sanarwar tafito ne daga bakin shugaban jam’iyyar APC Adams Oshiomhole, lokacin da mataimakin gwamnan jahar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna da tawagarsa suka kai wa masa ziyara a Abuja, ranar litinin 1 ga watan Yuli 2019.
Oshiomhole ya ce jam’iyyarsu mai mulki ta zabi Doguwa ne a matsayin shugaban masu rinjaye ne sakamakon jahar Kano sune suka bai wa jam’iyyar APC kuri’u masu yawan gaske fiye da kowa a zaben da ya gabata na 2019.