Alkali Binta ta bukaci EFCC ta bi umarnin kotu bisa belin Adoke

Babban kotun dake babban birnin tarayyar Abuja karkashin shugabancin Alkali Binta Nyako ta bada belin tsohon ministan shari’ar Najeriya wato Muhammad Bello Adoke

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC taki sakin Adoke bayan da ya cika sharrudan belin nasa na farko.

An kuma gurfanar dashi a babbar kotu Abuja ne a yau 10 ga watan Fabrairu 2020, bisa zargin yin almundahana da kudade.

Sai dai alkalin Binta Nyako ta bada belin nasa, inda ta bukaci EFCC ta su bi umarnin kotu bisa belin Adoke, kuma zata lara da sharrudan belin farko wanda Alkali Abubakar Kutigi na babbar kotun dake Gwagwalada a Abuja, inda aka gurfanar da Adoke tare da mutane 6 bisa zargin zamba ya bayar, sannan kuma ta umarci EFCC data kai fasfo din wanda ake tuhuma da yake gurin su zuwa kotun ta Gwagwalada.

Alkali kutigi ya bada belin kan naira miliyin 50, tare da mutun daya wanda zai tsaya masa, kuma ya kasance yana gida a yankin kotun, sannan sai dinga zuwa kotun tare da wanda ake tuhumar, ta kuma bukaci Adoke ya kawo fasfo dinsa.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Adoke ne tare da shugaban kamfanin man Malabu oil and Gas Limited, Aliyu Abubakar, da Rasky Gbinigie, na kamfanin Agip, kan laifuka 42 na rub da ciki da babakere.
EFCC ta yi zargin cewa Adoke ya karbi cin hancin naira miliyan 300 daga hannun Aliyu kan rijiyar man OPL 245.

Kotu ta dage karar zuwa 1 ga watan Agusta 2020 dan fara sauraron shari’ar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More