Alkalin kotun koli, Sylvester Ngwuta, ya mutu

Allah ya yi wa Mai Shari’a Sylvester Ngwuta, Alkalin Kotun Koli, rasuwa.
Majiyoyi a kotun kolin sun tabbatar da cewa Ngwuta ya mutu da sanyin safiyar Lahadi a cikin barcin da yake yi a gidansa da ke Abuja yana da shekaru kusan saba’in.
An ce Ngwuta yana shirin yin ritaya daga Kotun Koli a ranar 30 ga Maris, 2021, bayan ya cika shekaru 70 na ritaya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More