Alkawuran da gwamna Ganduje yayi na tafiyar da wa’adin mulki na 2

Gwamnan Jahar Kano Dakta  Abdullahi Umar Ganduje, yace zabada  ilimi Kyauta ga nakasassun da ke cikin Jahar a dukkannin matakai.

Bayyana hakane a wajen taron rantsar da shi wa’adin mulki karo na 2 a jahar Kano a ranar Laraba, 29 ga watan Mayu.

Ganduje ya yi alkawarin bayar da ilimi kyauta ga dukkanin yaran Jahar da suka isa shiga makaranta, kuma  za a yi  rangwame sosai ga ‘yan asalin Jahar da suke cikin manyan makarantun na jahar.

Ya kara da cewa, gwamnatin na shi za ta yi amfani da nasarorin da ta samu a zangonta na farko na sassan ilimi, noma, manyan ayyuka da kuma sashen lafiya.

Ya ce, zangon mulkin nashi na biyu zai samar da wata sabuwar hukuma mai suna, Kano State Small Town Water Supply Agency, wacce za ta kula da samar da ruwa ga al’ummomin da suke a karkara.

Gwamnan kuma ya yi alkawarin habaka noma a Jahar, yana mai karfafa daukaka matsayin kananan manoma, ya kuma sabunta aniyarsa ta yakar cin hanci da rashawa.

A karshe yace  zangon mulkin na shi na 2 zai tabbatar da farfado da hukumar hana cin hanci da karbar rashawa ta Jahar ta yanda za ta yi aikinta sosai, tare dayin alkawarin gudanar da gwamnatin da za ta kunshi kowa da kowa ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, inda yayi nuni da cewa, zamanin siyasa kuma ya  wuce a wannan lokacin.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More