Alvaro Morata yana dab da komawa Juventus 

Alvaro Morata yana dab da komawa Juventus 

 

Alvaro Morata yana dab da komawa Juventus a matsayin aro na tsawon kaka, wanda zai hada da zabin saye, kuma Bianconeri za ta gabatar da shi a ranar Laraba.

 

Juventus za ta biya Dollar miliyan goma ga Atletico Madrid don samu karbar aron shi.

Bayan da Atletico Madrid ta amince da bukatar Morata da ya koma Juventus sun hanzarta tattaunawa don sayen dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

 

A safiyar Talata, Morata zai yi gwajin lafiyarsa a Juventus, inda zai sake haduwa abokan nan taka ledar wanda ya hada da Andrea Pirlo a matsayin kocin sa.

 

A ranar Laraba, za a sake gabatar da dan wasan mai shekaru 27 a matsayin sabon dan wasan Juventus.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More