Amitabh Bachchan, Abhishek, Aishwarya Rai Bachchan da ‘yarta sun kamu da Coronavirus

Shahararriyar ‘yar fim din Bollywood Aishwarya Rai Bachchan da ‘yarta sun kamu da Coronavirus, kwana guda bayan sirikinta Amitabh Bachchan da mijinta Abhishek sun kamu da cutar.

Ministan lafiya na kasar, Rajesh Tope ne ya wallafa hakan a tuwita yana mai cewa Aishwarya da ‘yarta sun kamu da Coronavirus.

Sai dai ba a sani ba ko suma an kwantar da su a asibiti kamar yadda aka kwantar da Amitabh da mijin nata a ranar Asabar.

Masu dauke da cutar a India sun kai 850,000 ya yin da aka bayyana kamuwar mutum sama da 28,637 da suka kamu cikin awa 24.
.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More