An bai wa Ministan Neja Delta kwana biyu ya bayyana sunayen ‘yan majalisar da aka bai wa kwangila

Menene ra’ayinku game da hakkan?

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Femi Gbajabiamila ya bai wa Ministan Harkokin Yankin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, kwana biyu ya wallafa sunayen ‘yan majalisar da Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ta bai wa kwangiloli.

Femi ya bayar da umarnin ne a zaman majalisar na yau Talata, inda ya ce matukar ministan ya gaza yin hakan to majalisar za ta yi amfani da dukkanin karfin ikonta don tabbatar da ya yi hakan.

A jiya Litinin 20 ga watan Yuli ne Minista Godswill Akpabio ya fada wa kwamitin Majalisar Dattawa da ke bincike kan almubazzaranci da ake zargin NDDC da yi cewa mafi yawan kwangilar da hukumar ta bayar ‘yan majalisar kasa aka bai wa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More