An bude makarantu a kasar China inda Coronavirus ta fara barkewa

Rayuwar yau da kullum ta dawo a China, kasar da aka fara samun barkewar cutar Covid19 da yanzu ta mamaye duniya

An fara bude makarantu a manyan biranen China bayan shafe lokaci suna rufe saboda annobar Coronavirus

Dalibai sun koma makarantu a biranen Beijing, Shanghai da Hangzhou ko da yake ba dukkaninsu ba ne amma daliban da za su rubuta jarabawar shiga jami’a aka amince su dawo karatu.

Sai dai makarantu a Wuhan inda cutar ta barke za su ci gaba da kasancewa a rufe.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More