An bukaci na tsige Sarki Sanusi daga karagar mulki – Ganduje

An bukaci Gwamnan jahar kano dakta Abdullahi Umar Ganduje da ya gaggauta fara shirin tsige Sarkin Kano Muhammdu Sanusi II, domin kare doka da oda da kuma ikon da masu zabe na jahar suka ba shi.
Babban Sakataren yada labarai na gwamnan Abba Anwar, ya fitar da sanarwar hakkan ne a ranar Alhamis, inda ya bayyana cewa, wata gamayya ta kungiyoyin farar hula 35, karkashin sunan UMBRELLA OF KANO CONCERNED CIVIL SOCIETY GROUPS, suka bukaci hakan a wata wasika da suka aika wa gwamnan, wanda shugaban gamayyar kungiyoyin Kwamared Ibrahim Ali ne ya rattaba hannu a wasikar.
A sanarwar sakataren ya bayyana cewa gamayyar kungiyoyin ta ce tana lura tare da nazarin yadda al’amuran jahar suke kasancewa musamman a wannan lokaci, dangane da rashin jituwa da ake yi tsakanin gwamnatin jahar da kuma Sarkin Kanon.
Sanarwara ta ce kungiyoyin sun tunatar da shi game da abubuwan da suka bijiro bayan da babbar kotun jahar Kanon ta soke dokar Majalisar Sarakunan Gargajiya jahar, wadda Majalisar Dokokin jahar ta yi.
Hukuncin da a karshe ya bayar da damar yin wata sabuwar dokar, da ta kai ga kirkiro Karin masarautu hudu masu daraja ta daya, dokar da kuma ta ba wa gwamnan damar daukar matakin ladabtar da duk wani sarki da ya saba mata.

Kungiyoyin sun nuna takaicinsu da matakin shari’a da aka ce wai masu nada sarki daga daya daga cikin masarautun biyar da dokar ta kafa suka kalubalanta.

Anwar ya ce wasikar ta kuma nuna takaicin yadda wadanda ke kiran kansu dattawan jahar, tare da sukar cewa an yi dokar ne da nufin bata tarihin masarautar Kano na shekara 1000, suka shigar da karar ta biyu.
Jami’in ya bayyana a sanarwar mai dauke da sa hannunsa cewa bayan da gamayyar kungiyoyin ta bayyana dukkanin fannonin da ake da sabanin, ta ce abin da Sarkin Kanon yake yi na kin martaba gwamnatin jahar Kano da hukumominta,ba kawai ya saba wa tsarin mulki ba, wani yunkuri ne na yi wa gwamnatin kishiya, wanda suka ce ba wani shugabanci da ya san abin da yake yi da zai lamunta da hakan, ya bari ya ci gaba.
Ya ce ‘yan kungiyoyin sun kuma yi watsi da ikirarin masu kiran kansu dattawan Kanon wadanda ke neman haifar da rudani.
Wasikar gamayyar a cewar sanarwar Babban Sakataren yada labaran na gwamnan na Kano ta yi kira ga gwaman jahar da ya hanzarta tabbatar da ganin Majalisar Masarautun ta fara aiki, sakamakon hukuncin babbar kotun jahar na kwanannan.
Sanarwar ta kuma bayyana cewar, kungiyoyin tace, idan Sarkin Kanon ya ki yin biyayya ga gwamnatin Kano, to sun bukaci gwamnan da ya hanzarta yin amfani da tanadin dokar Masarautun ta 2019, wajen sama wa jahar ta Kano cigaba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More