An damka wasu mutane hudu da ake zargi dillalan man fetur ba bisa ka’ida ba ga EFCC a Uyo

Ofishin shiyya na Uyo na Hukumar Yaki da Cin Hanci da Ta’annati da Dukiyar Kasa, EFCC, ya karbi ragamar binciken wasu mutane hudu da ake zargi dillancin mai ba bisa ka’ida ba.
J. Shenu, Kwamandan sansanin sojojin ruwan Najeriyar J Shenu, ne ya damka . wanda ake zargin tare da durarrrukan ma 35 masu cin lita 300 da jiragen ruwa guda biyu na katako da kuma jirgin ruwa na fiber daya da aka gano daga hannunsu.
An kama mutanen hudun da ake tsargi : Yomi Philip Omoshola, Fayowola Ogunfunyi, Japheth Emmanuel Pius da Ofonime Bassey Eniefiok a wasu samame biyu da aka kai hanyoyin ruwa na Effiat da ke Ibaka.
Yayin da aka kama Yomi Philip Omoshola, Fayowola Ogunfunyi tare da furarrukan mai ashirin da shida masu cin lita 300 a cikin kwale-kwale biyu na katako na kirar gida.
Japheth Emmanuel Pius da Ofonime Bassey Eniefiok an cafke su ne da ganga tara mai cin lita 300.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More