An fitar da Maman Daura ganin likita kasar waje

An fitar da dan’uwan shugaba Muhammadu Buhari kuma amininsa, Alhaji Mamman Daura, kasar Birtaniya don ganin Likita bisa da rashin lafiyan da yake fama da ita.

An fitar da Mamman Daura ne a jiya Laraba 19 ga watan Agusta 2020, kasar waje cikin jirgi na musammam, sakamakon yana fama da matsalar numfashi da wasu alamomin kamuwa da annobar cutar Covid19 tun ranar Juma’a kamar yadda jaridun Najeriya suka rawaito.

A cewar wasu, tsohon dan jaridan kuma babban aminin Buharin yana fama matsalar koda kuma ya kan ziyarci turai don ganin Likita.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More