An gurfanar da Adoke a kotu bisa tuhume-tuhume 42

An gurfanar da tsohon ministan shari’ar Najeriya Mohammed Adoke a ranar alhamis 23 ga watan Janairu 2020 a babbar kotun tarayya da ke Gwagwalada Abuja.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC ta gurfanar dashi a gaban kotun kan  tuhume-tuhume 42 da wasu mutane shida da ke da nasaba da badakalar dala biliyan 1.09 na man Malabu.

Sauran da ke fuskantar shari’a sune: Nigeria Agip Exploration Limited(ENI) Shell Nigeria Ultra Deep Limited, Shell Nigeria Exploration Production Company Limited, Malabu Oil and Gas Limited, Aliyu Abubakar da kuma Rasky Gbinigie.

Kotun karkashin alkali Idris Kutige ta dage zaman zuwa 27 ga watan Janairu 2020.

A ranar ne a sa ran shigar da maganar belinsu duka, bayan da suka ki amince wa da tuhume-tuhume da EFCC din ke yi masu.

Sai dai Bala Sanga wanda lauya ne na EFCC yace, son samu a bar maganar belisu nasu, har sai a gama gudanar da duk wani bincike a kan su tare da yanke hukucin shari’ar, kafin sanin matsayar belin nasu.

EFCC za’a cigaba da tsare Adoke a zuwa ranar Litinin.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More