An kaddamar da sabuwar kotun daukaka kara a jahar Kano

Gwamana jahar Kano dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci taron kaddamar da kotun daukaka kara reshen jahar Kano a ranar Litinin 10 ga watan Fabrairu 2020, wanda Gwamnatin sa ta gina bisa amincewar shugabar kotun daukaka kara ta kasa wato Justice Zainab Bulkachuwa, wadda ta kaddamar da sabuwar kotun tare da sauran manyan alkalan kotun na kasa.

Bayan kaddamarwar ne kotun tayi zaman farko, inda ta saurari kararraki guda uku, wanda da ya kamata a saurara a kotun daukaka kara ta Kaduna.
Kashi 80% na kararrakin da aka kai kotun Kaduna duk sun fito ne daga jahar Kano da kuma Jigawa,sakamakon hakan ne ya sanka aka dawo, da takardun da aka shigar kotun ta Kaduna zuwa sabuwar kutun ta Kano.

Taron ya samu halartar Gwamnan jahar Jigawa Abubakar Badaru, alkalan kotun daukaka kara, mayan jami’an gwamnatin da ma dai sauransu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More