An kafa jam’iyyar Democratic Party of United States a rana irin ta yau

Rana mai kamar ta yau – ko kun san a rana mai kamar ta yau 8 ga Janairu aka kafa jam’iyyar siyasar nan da tafi kowacce jam’iyyar siyasa a fadin duniya dadewa tana nunfasawa?

• A rana mai kamar ta yau 8 ga Janairu, 1828 aka kafa jam’iyyar Democratic Party of United States wadda aka fi sani da Democrats.

Jam’iyyar Democrats ita ce jam’iyyar da tafi kowacce jam’iyyar siyasa dadewa tana nunfasawa a duniya. Jam’iyyar ta shafe kimanin shekaru 191 ba tare da ta taba rushewa tun lokacin da aka kafa ta.

Tun daga kafata, jam’iyyar ta samar da shugabannin kasar Amurka 15;

Andrew Jackson, shugaban kasar Amurka na 7

Martin Van Buren shugaban kasar Amurka na 8

James K. Polk, shugaban kasar Amurka na 11

Franklin Pierce, shugaban kasar Amurka na 14

James Buchanan, shugaban Amurka na 15

Andrew Jackson, shugaban kasar Amurka na 17

Grover Cleveland, shugaban kasar Amurka na 22 da 24

Woodrow Wilson, shugaban kasar Amurka na 28

Franklin D. Roosevelt, shugaban kasar Amurka na 32

Harry S. Truman, shugaban kasar Amurka na 33

John F. Kennedy, shugaban kasar Amurka 35

Lyndon B. Johnson, shugaban kasar Amurka na 36

Bill Clinton, shugaban kasar Amurka na 39

Barack Obama, shugaban kasar Amurka na 44.
Jam’iyyar na da magoya baya kimanin mutum miliyan 44,706349

A halin yanzu jam’iyyar dake zama mai adawa na da sanatoci 45 cikin dari, da yan majalisa 235 cikin 435, da gwamnoni 21 cikin 50.

• Haka zalika a rana mai kamar ta yau a 1912 aka kafa jam’iyar African National Congress ANC wadda su Nelson Mandela su kai gwagwarmaya a cikinta har sai da su ka yi nasarar kawo karahen wariyar launin fata a kasar Afrika ta Kudu.

• A rana mai kamar ta yau a1926 aka nada Abdul Aziz ibn Saud a matsayin shugaban kasar Hijaz wadda a yanzu ake kira da Saudiyya.

• A rana mai kamar ta yau a 1984 shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim jong In

• A rana mai kama ta yau a 1967 aka haifi shaharraren mawakin nan na Amurka Robert Sylvester Kelly wanda aka fi sani da R. Kelly

• A rana mai kama ta yau a 1986 aka haifi dan wasan tsakiyar Manchester City da Kaspar Spain David Silva

• A rana mai kama ta yau a 1992 aka haifi dan wasan bayan Atletico Madrid da kasar Spain Koke.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More