An kama kishiyoyi da uban yaron da aka daure a turken awaki

Gwamnatin jahar Kebbi ta ba da umarnin gudanar da binciken  gaggawa kan abin da ta kira ‘rashin imanin rikon sakainar kashin da aka yi wa wani yaro’, dan kimanin shekaru 10 mai suna Jibril Aliyu.

Jami’an hukumar kare hakkin dan’adam suka kubutar da Jibril yana tafiya da kyar saboda sirancewa.

Barrista Hamza Attahiru Wala na hukumar kare hakkin dan’adam ya ce “sun samu Jibril Aliyu ne daure a rumfar awaki, yana cin kashi busashe na dabbobi, harda nashi,  ko magana baya iya yi”inda suka yi magana da matan (gidan) suka ce eh yaron bai da hankali”
Lauyan ya shaida wa BBC cewa iyayensa sun yi iƙirarin cewa Jibril Aliyu na da farfaɗiya kuma ba shi da hankali. “Amma mu hay yanzu ba mu gani ba”.

Sai dai a wani bidiyo an ji ɗaya daga cikin kishiyoyin babar Jibril na musanta zargin ɗaure yaron. Ta yi rantsuwar cewa wallahi tana ba shi abinci.

Mai magana da yawun gwamnan jahar Kebbi, Aliyu Bandado Argungu,  ya ce binciken zai yi kokarin bankado sanadi da kuma gazawar mutanen da suka kamata su kare rayuwar kananan yara da ma manya a jahar.

Gwamna Abubakar Atiku Bagudu ya bayyana takaici da damuwa kan yadda Jibril ya shiga garari ba kawai a hannun iyayensa ba, har ma da gazawar makwabtansu da ma daukacin harkokin gudanawar gwamnati.

Kuma a wani sako da ta wallafa a shafinta na tiwita, gwamnatin Kebbi ta ce za ta dauki nauyin kula da lafiyar yaron da kuma dawo da shi cikin hayyacinsa.

A cewarta, kishiyoyin babar Jibril ne da mahaifinsa suka daure shi a turken awaki tsawon shekara biyu a unguwar Badariyya cikin Birnin Kebbi kafin kubutar da shi a ranar Lahadi.

Sai dai a wani bidiyo an ji ɗaya daga cikin kishiyoyin babar Jibril na musanta zargin ɗaure yaron. Ta yi rantsuwar cewa wallahi tana ba shi abinci.

Tuni dai ‘yan sandan jahar Kebbi suka ce sun tsare uban Jibril tare da matansa uku don ci gaba da bincike kan dalilin da ya sa aka bar shi cikin mummunan yanayi tsawon lokaci.

DSP Nafi’u Abubakar ya ce “Eh to, alhamdulillahi! Yanzu haka yana asibiti shi yaron…. muna so mu ji sakamakon asibiti me ze nuna ko rashin abinci ne da tsagwamawa suka sa shi halin da yake ciki”.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More