An kashe Mutane 44 Ciki Har Da Yan Sanda 4 A Sabbin Hare-haren yan Bindiga

An kashe ‘yan sanda biyu yayin wani hari a Hedikwatar Shiyya da ke karamar hukumar Ebonyi, yayin da wasu ‘yan fashi suka kashe wasu biyu yayin wani hari da suka kai ofishin ‘yan sanda na Magami da ke cikin Karamar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara.

A kalla mutum 44 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da aka samu a jihohi takwas tsakanin Juma’a da safiyar Lahadi,ciki har da yan sanda 4 sakamakon hare-haren da wadanda ake zargi yan haramtacciyar kungiyar yan aware ta IPOB ke kai wa jami’an tsaro da kadarorin gwamnati.
An kashe ‘yan sanda biyu yayin wani hari a Hedikwatar Shiyya da ke karamar hukumar Ebonyi, yayin da wasu ‘yan fashi suka kashe wasu biyu yayin wani hari da suka kai ofishin ‘yan sanda na Magami da ke cikin Karamar Hukumar Gusau ta Jihar Zamfara.
An kuma yi garkuwa da mutane 14 a jihar Kaduna. ‘Yan bindiga sun kashe akalla 21 a hare-haren da aka kai kan al’ummomin Zamfara da wasu 12 a Neja.
Sun kuma kashe 3 a Sakkwato kusan lokaci guda. Mutuwar mutum 21 sai Niger da ke biye mata da 12. Filato ta dauki rayukan mutane biyar; Sokoto uku; Adamawa biyu yayin da Ebonyi, Delta da Edo suka sami mutuwar mutum 1 kowannensu.
An kuma kashe wasu mutane uku da ake zargin masu satar mutane ne bayan da wasu gungun ‘yan banga suka afka wa wata kasuwa a Jihar Adamawa bayan da aka samu labarin kasancewar masu garkuwar.
An ce masu garkuwar sun yi tirjiya inda kuma an kashe su har lahira ta hanyar cinna musu wuta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More