An kwalla rana mafi zafi data kai digira 54.4 ma’aunin salshiyas a Death Valley

Ana kwalla rana mafi zafi da ba a taba irinta ba a duniya a gandun daji na Death Valley a yakin Lassen a jahar California da ke Amurka a ma’aunin 54.4 na salshiyas, wanda ya haddasa guguwa mai dauke da wuta a ranar Asabar.

Hukumar Kula Da Yanayi ta Amurka ce ta tabbatar da hakan.

A baya an taba samun tsananin zafi a digiri 54 ma’aunin salshiyas a yankin na Death Valley a shekarar 2013.

Sannan haka kuma Christopher Burt, masanin tarihin yanayi ya ce
a shekarar 1931 an samu wani zafin yanayin a digiri 55 na ma’aunin salshiyas a Tunusiya, sai dai
an samu hakan ne a lokacin mulkin mallaka don haka babu sahihanci kan batun.

Hoto daga BBC

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More