An nada sabon kwamishinan yansanda a Kano

Babban sufetan Yansandan Najeriya, Mohammed Abubakar Adamu ya aika da sabbin kwamishinonin Yansanda zuwa wasu jahohin Najeriya guda 7 domin samar da ingantaccen tsaro a cikin jahohin da kewayensu.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa babban sufetan ya dauki mataki ne sakamakon karin girma da wasu kwamishinonin yansanda suka samu, wato mukamin mataimakin sufetan yansanda(AIG).

Kakakin rundunar Yansandan Najeriya Frank Mba, ne

ya fitar da  sanarwa hakkan a ranar Alhamis, inda yace nadin mukaman ya fara aikin ne a take, tare da fadar sunayen sabbin kwamishinonin da jahohinsu kamar haka;

  • Habu Sani Ahmadu jahar Kano
  • Phillip Sule Maku jahar Bauchi
  • Lawal Jimeta jahar Edo
  • Imohimi Edgal jahar Ogun
  • Nkereuwem A Akpan jahar Cross Rivers
  • Odumusu Olusegun jahar Legas
  • Kenneth Ebrimson jahar Akwa Ibom

Babban sufetan ya yi kira ga sabbin kwamishinonin da su tabbata sun daura daga inga magabatansu suka tsaya musamman wajen samar da tabbataccen tsaro a jahohin da aka turasu su yin aikin, su kuma yi aiki tare da sauran masu ruwa da tsaki a jahohin don samu cigaba  tare da cimma manufar tasu.

Daga karshe babban sufetan Yansandan ya nemi al’ummar jahohin guda bakwai su baiwa sabbin kwamishinonin hadin kai tare da goyon baya domin tabbatar da tsaro tare da kare dukiya da rayukansu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More