An nada sabon mai kula da lafiya shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Aliyu Musa a matsayin babban jami’i mai kula da lafiyarsa.

Mai magna da yawun shugaban, Garba Shehu  ne ya fitar da sanarwar hakkan a  shafinsa na Twiter  a yau litinin 29 ga watan Yuli 2020.

Sanarwar na cewa,  Musa dan asalin jahar Niger ne kuma kafin nadinsa ya yi aiki ne a Zone 5 na Benin City. “An nada Musa ne bayan an yi wa magabacinsa, Kwamishinan ‘Yan sanda, Abdulkarim Dauda sauyin wurin aiki.” Dauda yana daya daga cikin jami’an tsaron da aka yi wa canjin wurin aiki bayan harbe-harben da aka yi a fadar shugaban kasa da ya shafi masu tsaron matar shugaban kasa wato Aisha Buhari

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More