An Nada Shugaban Hukumar Kula Da Gajiyayyu Ta Najeriya

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da nada shugabannin sabuwar hukumar kula da masu larura ta musamman na kasar.

Tsohon dan majalisar wakilai daga Jahar Kebbi, Husseini Suleiman Kangiwa shi ne sabon shugaban hukumar, inda  aka nada Abba Ibrahim daga Arewa Maso Gabas a matsayin Sakatare.

An kafa sabuwar hukumar ta kula da masu nakasa da ke bukatar kulawa ta musamman ne bisa tanadin dokar yaki da kyamar masu nakasa ta shekara 2019.
Wannan hukumar na da manufar kula da masu larura ta musamman da yawan su ya kai miliyan 25 a Najeriya, ta hanyar samar da karin kashi 5 cikin dari na aiyukan yi, da kuma ba su kulawa ta musamman akan batutuwan da suka dame su a dukan fanoni na rayuwa da kiwon lafiya da kuma harkokin walwalarsu da nufin share masu hawaye.

VOA ta rawaito cewa, Daya daga cikin shugabanin kungiyoyin masu larurar na kasa sakamakon cutar shan inna Misbahu Lawal Didi ya ce yanzu ne masu fama da nakasa za su fara samun damar shiga a dama da su a harkokin mulki a Najeriya.

Misbahu ya yaba da wanan kokari da Gwamnati ta yi, wanda ya ce dama sun dade suna jiran irinsa, domin baiwa mutanensu damar ba da ta su gudummuwa a harkokin cigaban kasa, wanda hukumar za ta taimaka masu gaya wajen cimma wannan burin.

Shugabar mata masu larura a kasar, Rabi Yusuf Gezawa, ta ce za su ci gaba da fafutukar tabbatar da ba a bar mata a baya ba a wajen cin gajiyar hukumar.

Rabi Gezawa ta ce sun fito kwansu da kwarkwata a kokarin ganin an samu Hukumar ta kula da masu bukata ta musamman duk da cewa suna da aure inda ta yi rokon kar maza su danne su a yanzu da kwaliya ta biya kudin sabulu.

Mashawarci na musamman ga shugaban kasa a lamurran masu larura ta musamman Shehu Garba, ya shawarci ‘yanuwansa da su sakawa wannan kokari na Gwamnati ta hanyar yin addu’o’i da fatan alheri.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More