An saki  Maina daga gidan  kurkuku dake  Kuje Abuja

Kotu ta bada umarnin sakin tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho na Najeriya garambawul, Abdurrasheed Maina, bayan ya shafe tsahon watannin  9 a tsare.

Daya daga cikin lauyoyin dake kare Mainai, Ademola Adedipe ya tabbatar wa da manema labarai hakkan a ranar Talata.
Tun ranar 26 ga watan Nuwamban 2019, kotun tarayya da ke Abuja a karkashin jagorancin mai Shari’a, Okon Abang ta bayar da belin Abdulrashid Maina, amma rashin cika sharrudan bayar da shi beli suka sa aka cigaba da tsare shi a kurkuku.
Daga bisani lauyoyinsa suka roki a sassauta masa sharrudan belin, inda alkali ya yarda ya rage yawan Sanatoci da za su karbi belin sa zuwa guda daya.

Sharrudan belin na Maina bai cika ba, sai da Sanata Mohammed Ali Ndume mai wakiltar yankin da Maina ya fito ya tsaya masa sannan aka bada belin sa ranar Juma’a 24 ga wannan wata na Yuli da misalin karfe 6 na yamma.
Sannan ba’a  sake shi ba, sai da aka cika wasu takardu wajen bin wasu hanyoyi da ka’idojin.

Rahoto ya nuna cewa, za a cigaba da shari’ar idan kotu ta dawo hutu a cikin watan Satumba mai zuwa.

Ana zargin  Maina da yin sama da fadi da naira biliyan biyu cikin kudin yin garam bawul wa tsarin fanshon Najeriya.
Hukumar EFCC ce dai ta gurfanar da Maina a gaban kotu bisa tuhuma 12, inda ya musanta zargin hakkan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More