Harbe-harben Lekki Toll Gate: An sallami mutum 3 daga asibiti cikin 30 da suka samu raunuka

Wannan shine mafi mummunan  dare daga cikin rayuwar mu, kasancewar lamarin ya wace karfin ikon mu, wanda hakan ya kafa mana mummunan tahiri, amma zamu fuskanci lamarin kuma mufito ta karfin mu, inji Gwamnan jahar Legos Babajide Sanwo-Olu bayan ya ziyarci  majinnata a asibiti, da zuka  fada iftila’in harbe- harbe da aka yi a Lekki tollgate na jahar Legos, a daren ranar Talata 20 ga watan Ocktoba 2020

A matsayina na gwamnan Jahar mu na gano cewa, komai zai kare a teburina, zan yi aiki da gwamnatin tarayya wajen ganin an shawo kan mummunan lamarin dake faruwa tare da tabbatar da jami’an tsaro suyi aikin su na kare rayuka da dokiyoyin al’umma. Inji gwamna Sanwo-Olu

Gwamnatin Jahar ta Legos ta kuma tabbatar da cewa mutane 30 sun samu raunuka, a iftala’in harbe-harbe da ya afku a Lekki Toll Gate, wanda ake zargin jami’an tsaro da bude wuta ga masu gudanar da zanga-zangar ta ENDSARS a daren ranar Talata.

Marasa lafiyan 10 na babban asibitin jahar, inda 11 ke asibitin Reddington, 4 a asibitin Vedic, ana kokarin kula da wayanda suka samu raunukan, yayin da mutane 2 ke karbar kulawa da musamman.

An sallami mutane 3 cikin mutane 30 da suka jigatan, sannan gwamnan yace zasu cigaban da bibiyan yanayin da marasa lafiya ke cikin don tabbatar da dukkanin su sun samu kulawar da ya dace.

#oaktvhausa #EndSARSBrutality #EndSars #Nigeriannews #oaktvonline

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More