Ana cigaba da neman mutane 5 cikin ruwa sakamkon hatsari

Iftila’in hadarin ruwa a tekun legos da ya afku bayan kwana shida, hukumar lura da ruwan na jahar Legas ta  bayyana cewar har izuwa yanzu ana neman mutune  biyar cikin ruwan ba’a zame ba, wayanda  tsautsayin ya afka dasu.

Oluwadamilola Emmanuel shi ne ya sanarwa manema labarai a ranar 4 ga watan Yuli a birnin Legas, cewa sun samu gawarwakin mutune 12 a gudanar da binciken gawarwakin a ruwan.

Sannan ya kara da cewa  suna nan  suna ci gaba da bincike domin gano sauran mutanen da ba’a gani ba, tare da  hadin guiwar hukumomin LASWA, LASEMA, jami’an ‘yan Sanda da ke kula da ruwan, da sauran hukumomi wajen ci gaba da binciken.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, hatsarin ya auku ne da misalin karfe 10 na daren ranar Asabar 29 ga watan Yuni a hanyar Badore-Ijede, sai dai mutane 3 sun samu nasarar kubucewa daga iftalin hatsarin ruwan.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More