Anyi gobara a ofishin INEC na Ondo

Gobara ta kone na’urorin tantance masu zaɓe a ofishin INEC a Ondo

Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya wato INEC ta fitar da sanarwar cewa babban ofishinta dake jahar Ondo ya kama da wuta

Gobarar ta faru ne daren ranar Alhamis a ofishin hukumar, inda kuma ta kone na’urorin tantance masu zabe a cikin kwantenar da aka ajiye su.

Sanarwar da hukumar INEC ta fitar a shafinta na Twitter ta ce jami’an kashe gobara sun yi kokarin kashe gobarar lokacin da ta tashi.

Hukumar ta kuma ce tana gudanar da bincike domin gano abunda ya haddasa tashin gobarar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More