APC ta bukaci PDP ta bayana dagantarsu  da Hushpuppi

Jami’iyyar APC ta bukaci hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC da kuma hukumar leken asiri kan hada-hadar kudi wato NFIU su bincike wasu manyan ‘yan jam’iyyar PDP.

APC ta yi kiran ne bayan hotunan wasu jiga-jigan ‘yan jam’iyyar ya karade shafukan sada zumunta inda aka gansu tare da Ramoni Igbalode wanda aka fi sani da Hushpuppi.

A ‘yan kwanakin nan ne dai aka kama Hushpuppi a Dubai bisa zargin damfara da almundahanar makudan kudade.

Jam’iyyar APC a Najeriya ta ce ya kamata a binciki Atiku Abubakar,  Bukola Saraki,  kuma tsohon Kakakin Majalisar Wakilai,Yakubu Dogara da kuma tsohon Sanata, Dino Melaye bisa alakarsu da Hushpuppi.

Sai dai mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbodian ya shaida wa BBC cewa har yanzu jam’iyyarsu ba ta zauna ta tattauna kan wannan zargin da ake yi musu ba.

APC ta bayyana cewa manyan ‘yan jam’iyyar ta PDP sun dauki hotun  da Hushpuppi a gidansa a lokacin da suka ziyarci Dubai, a wata sanarwa da mataimakin sakataren watsa labarai na jam’iyyar ta APC, Yekini Nabena ya fitar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More