APC ta gargadi masu neman EFCC ta binciki Tinubu

Kungiyar wayar da kan matasan ta jam’iyyar APC a Najeriya ta yi kira ga babbar jam’iyyar hamayya wato PDP da ta yi wa ya yanta gargadi kan su daina huro wuta ko zabani hakkan, wanda suke ikirarin cewa a binciki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar  ta APC National Awareness for Youth Vanguard ta fitar da sanarwar ne a ranar Laraba 13 ga Watan Nuwamba 2019, inda ta soki kiran da ake yi wa hukumar EFCC ta bi ta kan Jagoranta.

Shugaban kungiyar ta wayar da kan matasan APC Alhaji Mukhtar Abubakar, ya bayyana cewa ana neman EFCC ta binciki Bola Ahmed ne saboda ya bada gudumuwa wajen lallasa PDP a 2019. Wata kungiya mai zaman kanta, ta bukaci EFCC ta binciki abin da ya kai motar kudi cikin gidan Bola Tinubu a lokacin zaben da aka gudanar na shekara da muke ciki.

Sai dai Abubakar ya bayyana cewa , abun da ke faruwa shine, akwai wasu mutane da dama wayanda ke neman suna tare da sun haddasa fitina, kuma basu son hadin kan matasan Najeriya sobada wata bukatar su wacce baza ta  amfanawa al’ummar kasar tamu da komai ba.

“Irin wayannan ne  ke fitowa suna yin zargin a kan daya daga cikin ‘yan siyasan da ake ganin darajar a Najeriya a  yau.”

Abubakar ya shaidawa OakTV cewa , neman EFCC ta binciki Jagoran jam’iyyar APC saboda ya ajiye motar kudi a gidansa, tun kafin ayi nisa ba zai kai ga zuwa  ko ina ba, kuma ikirari hakkan bai da wani ma tabbata,domin babu wani wanda ya taba zargin hanyar arzikin na jagoran APC saboda da kansa ya miki kansa gaban Hukumar ta EFCC har sau 2 a lokacin da ya tsaya takarar gwamnan jahar Legas, bayan gabatar da adarorinsa a lokacin da ya ke mulkin jahar Legas.

A karshe Alhaji Mukhtar Abubakar yace, duk wani kamfani da dan siyasar Najeriya ya mallaka to babu shakka  al’ummar Najeriya suna sane da shi.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More