APC ta karyata zargin cewa DSS ta damke Oshiomhole

Jam’iyyar APC ta karyata zargin da ake na cewar   jami’an hukumar DSS sun cafke shugaban jam’iyyar ta APC  Kwamrade Adams Oshiomhole, kamar yadda ake rade radi a kafafen yada  labarai na kasa ta Najeriya.

LEADERSHIP A Yau ta ruwaito cewa, jami’an rundunar DSS sun cafke shugaban jam’iyyar APC din ne ranar Lahadi daddare sakamakon korafin da gwamnonin jam’iyyar suka yi na cewa, ya yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben fidda gwani da aka gudanar kwanannan.

Da yake mayar da martani a kan zargin cewa, shugaban jam’iyyar ya fuskanci tambayoyi daga jami’an DSS, Jami’in watsa labarai na jam’iyyar APC, Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana cewa, a halin yanzu Mista Oshiomhole ya yi tafiya zuwa kasashen waje, a saboda haka ba shi da lokacin da zai bata na mayar da martani a kan wannan rade radin.

Ya kuma kara da cewa, shugaban jam’iyyar, Kwamrade Oshiomhole, ya tafi kasashn waje ne ranar Litinin don gudanar da harkokin kashen kansa, ya kuma ki yin karin bayani a kana bin dake tattare da tafitar nasa.

Inda  a karshe yke cewa  radin, shugaban jami’iyyar baya  cikin kasar balle ya gaskata ko kuma ya karyata labarin.

 

You might also like More from author

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Comment moderation is enabled. Your comment may take some time to appear.