APC tayi watsi da matakin INEC kan zaben Bauchi

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta bayyana matakin da hukumar INEC ta dauka kan sakamakon zabuka jihohin Bauchi da Ribas a zaman wanda ya saba wa doka.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, jam’iyyar ta ce ta yi fatali da amincewar da hukumar ta yi da sakamakon zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.

Shugaban jam’iyyar reshen jihar Bauchi Alhaji Ahmad Uba Nana ya shaidawa BBC cewa hukumar zabe ba ta da hurumin yin amai ta lashe musamman la’akari da cewa maganar da gaban kotu.

Alhaji Uba ya ce ba za su lamunci da matakin da  INEC ta dauka ba, domin kowa ya shaida abin da ya faru a karamar hukumar Tafawa Balewa da kura-kuran da aka samu.

Daga cikin dalilan da jam’iyyar ta bayar har da zargin cewa akwai alaka tsakanin wanda hukumar ta tura domin tantance gaskiyar abin da ya faru a yanki wato Festus Okoye da kuma Kakakin majalisar wakilan kasar Yakubu Dogara wanda dan jam’iyyar PDP ne kamar yadda Alhaji Ahmad Uba ke cewa.

To sai dai a bangare guda jam’iyyar PDP wadda ke kan gaba a zaben na jihar Bauchi ta ce matakin hukumar ya yi mata daidai.

Jam’iyyarta bayyana haka ne duk da cewa da farko ta shigar da kara kotu ta na kalubalantar ayyana sakamakon zaben jihar a zaman wanda bai kammala ba da INEC ta yi da farko.

A tattaunawarsa da BBC shugaban jam’iyyar ta PDP a Bauchi Hamza Koshe Akuyam ya ce dama an riga an yi zabe kuma korafin da aka shigar an warwareta.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More