APC zata gurfanar da gwamnan Ishaku na Taraba a gaban kotu

Menene ra’ayinku game da hakan?

Babbar jam’iyyar hamayya ta APC a jahar Taraba da ke arewa maso gabashin Najeriya ta sha alwashin gurfanar da gwamnan jahar a gaban kotu idan bai mika mulki ga mataimakinsa ba.

Shugaban jam’iyyar ta APC, Ibrahim Elsudi ya ce sun bai wa Gwamna Darius Ishaku wa’adin mako guda ya mika mulki hannun mataimakinsa ko kuma su hadu a kotu.

BBC ta rawaito cewa APC na zargin gwamnan da kwashe fiye da tsawon wata biyu ba ya zaune a jahar, abin da ta ce ya zarce wa’adin da tsarin mukin kasar ya ba shi.

Sai dai bangaren gwamnan jahar ya yi watsi da barazana.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More