Asusun Lamuni na Duniya zai bawa Najeriya bashin $3.4b

Asusun Lamuni na Duniya wato IMF ya amince da bai wa Najeriya wani tallafin gaggawa domin taimakon kasar wajen yaki da cutar korona da kuma tayar da komadar tattalin arzikinta da ya ke yin kasa sakamakon faduwar farashin mai a kasuwar duniya.

Kudin da suka kai dala bilyan 3.4 su ne mafi girma da Asusun ya bai wa wata kasa da annobar korona ta dabaibaye.

BBC ta rawaito cewa,asusun ya sanar da tallafin kudin ne a ranar Talata jim kadan bayan da majalisar dokokin Najeriyar ta amince wa Shugaba Buhari cin bashin dala bilyan 2.3 a cikin gida domin cike gibin kasafin kudin kasar da ya samu tawaya saboda faduwar farashin mai.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More