ASUU Na Yunkuri Kara Tafiya Yajin Aiki

Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU), ta ce, kada a zarge ta idan har aka samu wata matsala a tsarin karatun jami’o’in gwamnati na kasar nan, sakamakon rashin niyyar cika alkawarin yarjejeniyar shekarar 2018 da aka kulla a tsakaninta da gwamnatin tarayya.

 

Shugaban kungiyar, Farfesa Biodun Ogunyemi ya fadi hakan ne a lokacin da yake karin haske ranar Laraba a Abuja kan yarjejeniyar da ke tsakanin su da gwamnatin tarayya, da kuma maganar lamuntar  ba wa kungiyar kudi biliyan 25 da ministan kudi, Adamu Adamu ya fada.

 

Ogunyemi ya ce, wannan biliyan 25 din, bangare ne daga cikin alawus din kungiyar, wanda kuma an yi ka’idar za a biya kudin ne a tsakanin 15 zuwa 28 na Fabarairun shekarar 2019.

Sai dai haryanzu hakan bai wakana ba.

 

Duba da cewa daga lokacin da maganar kudin ta basu a kafafen yada labarai, daga lokacin tumtubar jin ta bakin ASUU kan kudin .

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More