Atiku Bagudu ya bukaci yan jahar Kebbi da su rika biyan kudin lantarki

Gwamnan jahar Kebbi, Atiku Bagudu ya bukaci  mutanen  jahar sa da su daure su yi   kokarin  wajen biyan rukunin kamfanin wutar lantar wato  KEDCO kudin wutar sakamakon amfana da wutar da suke yi a tsawon awanni 24 a duk fadin jahar.

Gwamnan  ya bukaci hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a birnin Kebbi sakamakon korafin da masu amfana da wutar lantarkin suka kai na cewa, an rage tsawon awanni da wutar ke kaiwa daga awanni 24 zuwa awanni 14.

Inda yayi kokarin ganar da  masu korafin cewa,yanzu sashen wutar lantarkin yana hannun ‘yan kasuwa ne. Don haka suna ba da wuta ne gwargwadon biyan kudin wutar da jama’a ke yi.

Da haka ya  tabbatar da cewa, idan har mutane suka gaza biyan kudaden wutan to tabbas kamfanin da ke kula da wutar lantarkin ba zai iya ci gaba da ba da wutar lantarki kamar yadda ya saba badawa a baya ba.

Bagudu ya kara da cewa, gwamnatin jahar ta kashe kimanin Naira Biliyan 3 daga shekarar  2016 zuwa 2019 wajen samar da Tiransifoma da kuma samar da wutar lantarkin a jahar.

Duba da  hadin guiwar KEDCO da TCN, har ya sanya jahar ke samun wutar lantarkin har na tsawon awanni 24.

Amma yanzu rashin biyan kudin wutar ne ya sa KEDCO ba za su iya ci gaba da ba da wutar lantarkin har na tsawon awanni 24 ba.

Wakili daga KEDCO Malam Sani Sakaba,  wanda aka yi  tattaunawar war dashi ya ce, Kamfamin ya yi kokarin ba da wutar lantarki har ta Naira miliyan 900, amma da kyar suke neman hada naira miliyan 300 daga masu amfana da wutar.

Sakaba, ya jinjinawa gwamnatin jahar bisa tallafin wata-wata da suke baiwa kamfanin wutar lantarkin.

A  karshe ya shawarci kwastamominsu a jahar da su rika biyan kudin wutar lantarkin domin tabbatar da sun ci gaba da amfana da wutar har na tsawon awanni 24 kamar yanda ake bukata.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More