Atiku ne yace zabe – Buba Galadima

Injiniya Buba Galadima ya ce jam’iyyar PDP ta ba Atiku Abubakar cikakken goyon bayan don ya kalubalanci zaben 2019 a gaban kotu.

Atiku Abubakar da jam’iyyarsa ta PDP sun yi watsi da sakamakon zaben 2019 bisa zargin an tafka magudi a zaben, kuma Atikun ya ce zai garzaya kotu.

Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta musanta cewa an tafka magudi a zaben.

A ranar Laraba  ne aka bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben Najeriya a karo na biyu, abin da zai ba shi damar ci gaba da mulki har zuwa shekarar 2023.

Buba Galadima ya ce sun yanke shawarar mara wa Atiku baya ne bayan da suka yi wata doguwar muhawara da dukkannin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP ranar Litinin.

Daga nan, ya ce daya daga cikin matsayar da suka dauka ita ce “ba da cikakken goyon baya ga Atiku Abubakar kan ya kalubalance zaben 2019.”

Buba Galadima ya kara da cewa suna da hujjoji da za su gabatar a gaban kotu da ke nuna cewa “sune suka ci zaben da aka gudanar a ranar Asabar 23 ga watan Fabrairu da ta wuce. Har ila yau, Buba Galadima ya yi zargin cewa dan takararsu yana fuskantar matsin lambar kan kada ya kai batun gaban kotu.

Ya ce hakan na faruwa ne saboda jam’iyyar APC tana tsoron hujjojin da za su gabatar a gaban kotu.

 

A karshe Buba Galadima dole a bai wa dan takarar shugabancin Najeriya wata Atiku Abubakar domin shi y ace zaben.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More