Atiku ya kalubanlaci karin kudin lantarki

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya ce karin kudin wutar lantarki da aka yi mataki ne da bai dace ba.

Atiku ya ce ba ya goyon bayan karin kudin na lantarki a yayin da yan Najeriya ke murmurewa daga radadin kullen  sakamakon Coronavirus.

 Kamata yayi a karfafawa yan Najeriya gwiwa, ba dai a yi watsi da  kalubalen da suke fuskanta ba, duba da cewa, yan Najeriya da dama sun
shafe watanni ba kudaden shiga kuma ba laifinsu ba ne. Kamar yadda ya fitar a shafinsa na Twitter a yau 3 ga watan Satamba 2020.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More