Ba a bayyana abunda yayi sanadin rasuwar kwamishinan na Sokoto ba

Gwamnatin jahar Sokoto ta tabbatar da rasuwar kwamishinan filaye da gidaje Surajo Gatawa.

Ya rasu ne a ranar Lahadi inda aka yi jana’izarsa bayan Sallar Magariba a Sokoto, kamar yadda mai taimakawa Gwamnan jahar kan harakokin watsa labarai Muhammad Bello ya tabbatar wa BBC.

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce ya rasu ne bayan gejeruwar rashin lafiya, sai dai ba a bayyana sanadiyya rasuwarsa ba a sanarwar.
Ya rasu ya bar mata uku da yara.

Marigayin mai shekaru 63 a duniya, ya taba wakiltar Isa da Sabon Birni a majalisar Tarayya tsakanin 1999-2007, sannan ya taba rike mukamin shugaban karamar hukumar Sabon Birni bayan ya yi kansila.
A Cikin kwanaki biyu jahar Sokoto ta yi rashin manyan mutanen da suka hada da tsohon karamin ministan Lafiya da kanin mahaifin gwamnan jahar ta Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More