Ba dole bane halartar jana’izar mahaifiyata idan zuwa na zai kawo matsala ga yan uwana – Nnamdi Kanu

Shugaban yan gwagwarmayar kafa yankin Biafra Nnamdi Kanu, bayyana cewa idan zuwan sa Najeriya jana’izar mahaifiyarsa zai sanya mutanen sa cikin wata matsala to ban ga dalilin da zai sa ya zoba, sannan kuma bai saka wani sarki ya roka masa gwamnatin dan a barshi ya shigo kasar ba.

Nnamdi  ya bayyana hukuncin da ya yanke dangane da shigowar shi Najeriya domin halartar jana’izar mahaifiyar shi.

Mahaifiyar Kanu dai ta mutu ne a cikin watan Agustan da ya gabata sai ba’a sanar mutuwar a lokacin ba, sai a kwanakin nan, inda  Nnamdi Kanu ya dora alhakin mutuwar mahaifiyarsa akan gwamnatin Najeriya, wajen bayyana cewar hukumar sojojin Najeriya ce ta ci zarafinta, har hakan yayi sanadiyar mutuwar ta.

Wakilin Muryar Amurya ya samu damar zanatawa da  Nnamdi Kanu kan al’amarin dan ji ta bakin nasa.

Ga zantawar tasu:

VOA: Kwanan nan wasu sarakuna sun bukaci gwamnati da ta kyaleka ka shigo Najeriya domin halartar jana’izar mahaifiyar ka, me zaka ce game da wannan?

Kanu: Mahaifiyata ta mutu ne sanadiyar cin zarafin ta da gwamnatin Najeriya tayi, dan haka bana bukatar kowa ya rokar mini gwamnati domin na shigo na binne mahaifiyata. Ba wai na damu da sai na zo bane idan har hakan zai yi sanadiyyar bacewa da mutuwar wasu daga cikin yan uwanmu. Ba zanyi duk wani abu da zai kawo matsala ga mutanen mu ba kawai akan wata jana’iza, ko ina Najeriya ko bana nan dole za’a binne mahaifiyata.

VOA: Wasu daga cikin masu kalubalantar ka sunce kana so a raba Najeriya ne kuma hakan ya sabawa doka irin ta Najeriya, me zaka ce game da haka?

Kanu: Tambayar a nan ita ce wanene ya kirkiri Najeriya? Najeriya ba ita ce ta kirkiri kanta ba, kasar Birtaniya ce ta kirkiri Najeriya. Da babu wani abu da ake kira da Najeriya kafin kasar Birtaniya ta zo. Abin da muke so shine, Najeriya ta koma kamar da a lokacin da turawan mulkin mallaka suka shigo.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More