Ba mu amince da karin kudin wutar lantarki ba- NLC

Kungiyar kwadagon Najeriya wato NLC ta yi Allah wadai da yunkurin kara farashin wutar lantarki da kamfanonin da suka sayi NEPA suka fara a  kasar ta Najeriya.

Sakataren NLC, Emmanuel Ugboaja, ya bayyana cewa ma’aikatan Najeriya ba zasu yarda da wannan sabon farashin ba, kuma baza su taba yarda da wani karin farashin wutan lantarki ba.

Muna adawa da hakan kuma NLC ta bayyana matsayarta a jawabin da ta saki bayan ganawar majalisar zantarwarta da ya gudana a jahar Kano. Hakazalika, Ugboaja ya bayyanawa jaridar Thisday cewa NLC bata amince da kokarin sake sayen NEPA daga hannun yan kasuwa da gwamnatin tarayya ke shawarar yi ba.

Rahotunni sun nuna cewa Hukumar duba wutan lantarkin Najeriya ta tabbatar da karin farashin wutan latarki da kamfanonin da suka siya NEPA wato Discos suka bukata a fadin tarayya.

Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Laraba a rahoton da ta saki mai suna ‘Duba farashin wutan lantarki tsakanin 2016-2018’ ga kamfanonin wuta.A yanda sanarwar ta bayyana  an fara aiwatar da wannan kari tun 1 ga Yulin 2019.

Kamfanonin sun bayyana cewa an yi wannan kari ne saboda rashin cin riba a bangarensu wanda ke hanasu cigaba da zuba kudi cikin kasuwancin.

A shekarar 2018, kamfanonin sunyi ikirarin cewa ba karamin asarar sukayi ba yayinda suke sayan wuta N80.88 amma su sayarwa jama’a a farashin N31.50, hakan na sasu faduwar N49.38 ga kowani kilon wuta.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More