Ba na nadamar barin Real Madrid – Bale

Gareth Bale ya ce ya kara samun kwarewa a lokacin da yake tare da Real Madrid kuma ba ya nadamar barin kulob din inda ya koma Tottenham.

Bale ya koma Spurs ne a matsayin aro tsawon kaka a farkon wannan watan, bayan barinsa Tottenham shekaru bakwai da suka shude.

Duk da cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen lashe Kofin Zakarun Turai hudu, Bale bai samu jituwa da kocin kungiyar ba Zinedine Zidane, ya buga wasanni 20 ne kawai a kakar wasan da ta gabata.

“Kamar yadda na fada, ban yi nadamar abin da na aikata ba, duk abin da wani ya fada, wannan ya rage nasu ra’ayin su kawai za su fada.

Tottenham ta kare a mataki na shida a Premier a kakar wasan da ya wuce, kuma dawowar Bale, kungiyar za ta samu karfin gwiwa don dawowa kan manyan kungiyoyi hudu da za su sami shiga gasar Zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More