Ba ni da tabbaci kan bidiyon Ganduje na karbar dala – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya nuna tababa kan bidiyon da aka wallafa, wanda ke nuna gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudade na Dalar Amurka a hannu wayan da ba san su waye ba.

Wata jarida ce a Najeriya ta wallafa bidiyon tare da ikirarin cewa cin hanci ne ake bai wa gwamnan Ganduje.

Shugaban ya ce bai san irin na’urar da aka yi amfani da ita wajen sarrafa bidiyon ba. “A ce kamar gwamnan Kano yana dariya yana karbar Daloli abin mamaki ne.”-In ji Buhari.

Muhammadu Buhari ya bayyana haka ne a lokacin wata muhawara da gidan talabijin na kasar NTA.

Sai dai shugaban ya ce yayi shiru ne bai ce komai a kan bidiyon ba kasancewar lamarin yana gaban kotu.

Wasu al’umma da kungiyoyi masu rajin yaki da rashawa a kasar sun dade suna sukar lamirin shugaban kasar na kin cewa uffan game da zargin karbar cin hancin da ake wa gwamnan.

Kungiyar nan mai fafutukar yaki da cin hanci SERAP, ta kai shugaban kasar kotu a baya, bisa dalilin kin tursasa hukumar EFCC ko kuma bangaren shari’a su binciki gwamnan na Kano.

Gwamnatin shugaba Buhari dai ta ce ta sanya yaki da cin hanci da rashawa a sahun gaba cikin matsalolin da take son magancewa a kasar.

Sai dai ‘yan adawa na zargin gwamnatin da nuna son kai a yakin da ta ce tana yi da cin hanci.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More