Babban Sufeton ’Yan Sanda na kokarin kara tabbatar da tsaro

Babban sufeton ‘yan sanda na kasa, Muhammad Adamu, ya tabbatarwa da al’ummomin sassan Arewa maso Yamma da Arewa ta tsakiya, cewa, rundunar ‘yan sandan tana yin aiki tare da Sojoji da sauran jami’an tsaro wajen ganin an kawo karshen kasha-kashen ‘yan ta’adda baki daya.
 
Kakakin rundunar ‘yan sandan na kasa, Mataimakin Kwamishinan ‘yan sanda, (DCP) Frank Mba, wanda shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ya ce, shugaban ‘yan sandan ya bayar da wannan tabbacin ne a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Jahar Kaduna.
 
Ya ce, shugaban ‘yan sandan yayi jawabin ne ga masu ruwa da tsaki na yankin da suka hada da, manyan jami’an gwamnati, shugabannin al’umma, shugabannin mata da sauran su, a lokacin da ya kai ziyarar gane wa idonsa yanayin tsaro a yankin.
 
Mba ya ce, Shugaban ‘yan sandan ya taya al’umman yankin jimami a kan harin da yan ta’addan suka kai masu, ya kuma yi kira da karin bayar da goyon baya daga al’ummomin yankin domin hukumomin tsaron da aka tura yankunan su sami nasarar gudanar da ayyukan su, ya yi nuni da cewa, sai ta hanyar bayar da gudummawa daga duk wadanda lamarin ya shafa ne za a iya sammun nasara a kan ‘yan ta’addan. 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More