Babban Sufeton Yan Sanda ya sanar da dakatar da sanya gilashi mai duhu a jikin motoci

Sufeto-Janar na ‘yan sanda Usman Alkali Baba ya sanar da dakatar da sanya gilashi mai duhu (tinted glass) a jikin motoci a fadin Najeriya.
IGP din ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin ganawa da manyan jami’an ‘yan sanda ciki har da kwamishinoni da DIG daga sassan jihohin.
Ya kuma umarci da a dakatar da ba da lambar mota ta leken asiri.
Wannan, a cewarsa,wasu bangarori ne na kokarin da ake yi domin dakile munanan matsalolin tsaro a duk fadin kasar.
Yayin da yake bayar da sanarwar, ya sake nanata cewa an haramta saka shinge a han hanyoyi a cikin kasar kuma ya yi gargadin cewa shugabannin kwamandoji dole ne su aiwatar da shi kuma su shiga cikin dabarun sintiri na hanya a matsayin madadin saka shingaye hanyoyin.
IGP din ya kuma yi magana game da kame manyan masu laifi.
A cewarsa, wasu manyan mutane da ake zargi a hannun ‘yan sanda sun hada da mambobin kungiyar IPOB, masu satar mutane, da kuma‘ yan fashi wadanda suka amsa aikata wasu manyan laifuka a ‘yan kwanakin nan.
Ya jaddada bukatar manyan jami’an ‘yan sanda su tabbatar da da’a a cikin hukumonisu.
Daga cikin nasarorin da rundunar ‘yan sanda ta samu a cikin watanni biyu da suka gabata sun hada da kame sama da mutum 600 da ake zargi ciki har da mutanen da ake zaton sun kai wa Gwamna Samuel Ortom hari a farkon Maris, bana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More