Babu makawa APC ce zata lashe zaben 2019 – Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomole ya tabbatar da cewa; idan har aka gudanar da sahihin zabe a kasarnan, to APC ce zata swamu nasara  lashe zaben a zaben da ke harowa na a ranar 16 ga watan fabrairu.

 

A sanarwar da Malam Lanre Issa-Onilu, Sakataren watsa labaran t APC din na kasa ya fitar, ya tabbatar da hakan ne a wani zama da kwamitin zartarwa  na jam’iyyar da aka gudanar a babban birnin tarayyar Abuja.

 

Issa-Onilu ya ce; zaman a wannan lokacin ya zama wajibi ne domin yin duba da shirye-shiryen zaben da ke gabatowa ,Ya ci ga da cewa; Oshiomhole shi ne ya jagoranci zaman, inda kuma zaman ya samu halartar Jagororin jam’iyyar na jahar, ‘yan takarkarun  Gwamna a karkashin jam’iyyar  ta APC da kuma Sakatarorin jam’iyyar na duk fadin kasar ta Najeriya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More