Babu Messi da Ronaldo a cikin ‘yan takarar gasar Zakarun Turai.

Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ba sa cikin jerin ‘yan takarar karshe na kyautar gwarzon dan kwallon Turai na UEFA a karo na farko cikin shekaru 10, Kevin De Bruyne da Robert Lewandowski da za su fafata don neman kyautar.

Mai tsaron ragar Bayern Munich, Manuel Neuer shi ma yana cikin wadanda za su fafata a kyautar, inda za a sanar da sabon wanda ya ci kyautar a farkon Octobe

Ronaldo, wanda a yanzu haka yake taka leda a Italiya tare da Juventus, ya karbi lambar yabon har sau uku, yayin da shahararren dan wasan na Barcelona Messi ya lashe wannan lambar yabo sau biyu.

UEFA ta fitar da sunayen yan takarar karshe na kyautar gwarzuwar shekara ta mata da kuma gwarzon koci na shekara, tare da Lucy Bronze, Pernille Harder da Wendie Renard wadanda aka zaba na farko, da Jurgen Klopp, Hansi Flick da Julian Nagelsmann a fafatawar gwarzon koci .

A halin da ake ciki, Lluis Cortes, Stephan Lurch da Jean-Luc Vasseur sune ke cikin yan takarar karshe na kociyan mata na shekara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More