Bacewar Dadiyata: Bamu da hannu ciki – Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin jahar Kaduna ta musanta batun da ke cewa tana da hannu  wajen bacewar matashin nan  mai suna Abubakar Idris Usman wanda aka fi sani da Dadiyata.

Wasu  wanda zuwa yanzu ba’a gano su waye ba su kayi awun gaba da Dadiyata,  shekara daya da ta wuce kenan a gidan sa dake Barmawa.

Rahotunnin sun nuna cewa Dadiyata yana kan hanyar sa ta zuwa gida da misalin karfe 1 na dare wasu yan bindiga suka yi awungaba dashi cikin motarsa mai  kira BMW,

Wanda kawo yanzu ba amo ba labarin shi bare kuma motar tasa.

Kwamishinar Shari’a ta Kaduna, Aisha Dikko ta bayyana cewa, gwamnatin  Kaduna bata da wata masaniya akan  inda Abubakar Idris Usman wanda akafi sani da Dadiyata yake.

 Aisha Dikko ta ce “‘yan sanda ne suke bincike kafin gwamnati ta shiga maganar,koma basu kawo wa ma’aikatarmu abunda  suka gano ba”

Gwamnatin ta Kaduna ta shigar da karar wasu mutane, kan maganganun da suke yi wanda ba gaskiya bane, wanda ka iya tado rigima a garin. Inda kuma ake cigaban da bin lamarin ta hanyar daya dace.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More