Bakin ciki da jimami muke ranar 29 ga watan Mayu – Kwankwaso

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana cewa  su ba sa murna da ranar rantsar da sabbin gwamnoni, wato  29 ga watan Mayu  2019 saboda “fashin mulki aka yi masu”.

Ya ce a jahar Kano ranar ta 29 ga watan Mayu ta kasance  ranar bakin ciki .

Sanata Rabi’u Kwankwaso ya kara da cewa abin da ya faru a lokacin zaben ranar 21 ga watan Maris da ya bai wa gwamna Abdullahi Umar Ganduje nasara ya zo masu da ba-zata.

Zaben Kano dai ya ja hankali bayan sanar da cewa zaben bai kammalu ba a ranar Asabar 9 ga watan Fabrairu.

Yayin da aka sake   gudanar da zabe a wasu mazabun kananan hukumomi 28 a jahar Kano.

A karshe Jam’iyyar APC ce  ta lashe zaben a rumfunan kananan hukumomi 27 , yayin da PDP ta lashe karamar hukumar Dala.

Hakan ya bawa Gwamna Ganduje samun nasarar kumawa a karo na 2.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More