Bamu kori Sanusi daga jahar Kano ba – Kwamishinan shari’a na Kano  

Kwamishinan shari’a na Kano jahar Kano kuna Antoni ganar, Ibrahim Muktar ya ce,gwamnatin jahar ba ta kori tsigaggen Sarki Muhammadu Sanusi na II daga jahar ba.

A wata hira da Muktar  yayi da Channels TV Sunrise Daily a yau Laraba 11 ga watan Maris, ya bayyana cewa, sakataren gwamnatin jahar ya yi jawabi dalla-dalla wajen fitar da  sanarwar tsige Muhammadu Sanusi sannan an nada sabon sarki a ranar Litinin din,

 amma babu inda tayi nuni  da cewa a  kore shi. 

Batun korarsa baya daga cikin shawarar gwamnatin jahar Kano.

Muna ta ji a kafofin watsa labarai cewa an kori tsohon sarki, wanda baya daga cikin hukuncin mu.Sai dai abun da na sani shine, an fitar dashi daga jahar Kano. Jami’an tsaro sun yanke shawarar fitar da Sanusi daga jahar Kano sakamakon rahotanni kwararru da suka samu. Inji shi.

 

A karshe  Muktar ya bayyana cewa, ba sabon abu bane fitar da tsigaggen sarki daga gari domin wanzar da zaman lafiya a jahar, wanda hakkan bai sabawa kundin tsarin mulki wacce ta bayar da yancin yawo ba.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More